'Yan bindiga sun kashe mutane 15 a Sanai

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gunmen kill 15 in Sanai

Hukumomi a Masar sun ce 'yan bindiga sun kashe a kalla mutane 15 a wani hari da suka kai a wuraren duba ababen hawa a yankin arewacin Sanai.

Dakarun tsaron kasar sun dade suna yunkurin murkushe 'yan ta'adda a yankin domin kawo karshen ta'addanci da munanan hare-haren da suke kai wa dakarun tsaro.

A 'yan kwanakin nan, 'yan ta'addan da suka fi kai munanan hare-hare sun yi mubaya'a ga kungiyar IS.

A wannan shekarar an hallaka mutane da dama a arewacin Sinai tsakanin sojoji da fararen hula.

A watan jiya, dakarun tsaron Masar sun yi ikirarin kashe 'yan ta'adda 70.