Ba na son a kara min wa'adi a INEC — Jega

Image caption Attahiru Jega ya ce babu sani ba sabo

Shugaban hukumar zaben Nigeria, Farfesa Attahiru Jega, ya ce ba zai amince da duk wani yunkuri na kara masa wa'adin aiki a hukumar ba.

A hirarsa da BBC, Jega ya ce ya taka irin tasa rawar, kuma ya kamata a bai wa wasu dama su jarraba.

"Alhamdulillah an nemi ni na ba da gudunmuwa domin ci gaba kasarmu kuma na yi iyaka kokarina. Duk aikin da mutum zai yi shekara biyar ni a gani musamman wannan aikin mai wuya, to idan aka yi aka gama lafiya to ya kamata a ba wani dama shi ma ya zo ya yi. Don haka ni ba na sha'awa ba na tunani kuma idan an nemi ni, ba zan yi ba Insha Allah," in ji Jega.

Ya kara da cewar "Irin wannan aikin idan mutum ya karbe shi dole ya yi shi Fisabilallah, ya tabbatar an yi shi cikin adalci kuma babu sani ba sabo. Alhamdullilah mun ji an yi wannan zaben kuma mutane sun yaba."

Kasashen duniya sun yaba wa Jega a kan yadda ya gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya cikin lumana da adalci.