'Yan bindiga sun kai hari a Kenya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan Al-shabab ne sun kai a Kenya

'Yan bindiga wadanda fuskokinsu ke rufe, sun kai hari harabar wata jami'a a arewa maso gabashin Kasar Kenya kusa da iyaka da Somalia.

An ji karar harbe- harben bindiga da kuma fashewar abubuwa daga jami'ar dake garin Garisa.

Dakarun Tsaron Kenyan sun yi musayar wuta tare da 'yan bindigar

Jami'ai sun tabbatar da mutuwar mutane biyu da kuma jikkatar mutane hudu.

Har yanzu dai ba a kaiga sanin wadanda ke da alhakin kai harin na baya bayan nan ba, amma mayakan al-Shabab na Somaliya sun sha kaiwa Kenyan hari a 'yan shekarun da suka gabata