'Yan bingida sun kashe mutane a Kenya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dalibai sun fice da jami'ar

Wasu 'yan bindiga da suka yi shigar-burtu sun kai hari a wata jami'a da ke arewa maso gabashin Kenya, kusa da kan iyakar kasar da Somalia.

An yi ta jin karar harbe-harbe a lokacin da 'yan bindigar ke kutsawa cikin jami'ar da ke garin Garissa.

An kashe masu gadin makarantar guda biyu.

Mutane da dama sun tsallake rijiya da baya koda yake an kai kimanin mutane 30 asibit sakamakon munanan raunukan da suka ji.

Wakiliyar BBC -- wacce ta je wurin da lamarin ya faru -- ta ce lamarin ya rutsa da dalibai da malamai da dama.

Jami'an gwamnati na can suna yin taro a kan batun, kuma tuni aka aika da manyan jami'an tsaro zuwa yankin domin shawo kan lamarin.

Har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin, sai dai kungiyar al Shabaab daga Somalia ta sha kai hare-hare a Kenya tun daga shekarar 2011 lokacin da kasar ta aike da dakarunta Somalia.