Tsohon shugaban 'yan sanda MD Yusuf ya rasu

Tsohon Sufeto Janar na 'yan sandan Nigeria, Muhammadu Dikko Yusuf ya rasu bayan doguwar jinya a Abuja.

Dan shekaru 83, MD Yusuf ya jagoranci 'yan sandan kasar daga shekarar 1975 zuwa 1979 a lokacin zamanin mulkin soji.

Jika ne ga tsohon sarkin Katsina, Muhammadu Dikko.

A zamanin mulkin margayi Janar Sani Abacha, MD Yusuf ne shugaban jam'iyyar GDM kuma ya taba rike mukamin shugaban kungiyar tuntuba ta arewa watau ACF.