Kasuwar hannayen jari ta daga a Nigeria

Image caption Darajar naira ta karu idan aka kwantata da dalar Amurka

Alkaluman kasuwar hannayen jari a Nigeria sun nuna cewa darajar kasuwar ta daga da kashi 8.33, wani lamari da ba a taba ganin irinsa ba,cikin sama da shekaru 53 da kafa kasuwar hannayen jari.

Masana tattalin arzikin kasa sun ce bunkasar kasuwar na da nasaba da nasarar da sabon zababben shugaban kasar, Janar Muhammadu Buhari ya yi da kuma hasashen da aka yi kasar za ta fada cikin rikici amma sai aka wanye lafiya.

Wani masani a kan harkokin kasuwar zuba jari, Mallam Kasimu Garba Kurfi, ya shaida wa BBC cewa "Gaskiya yadda aka aiwatar da zaben nan shi ne ya bai wa kasuwar mamaki, saboda ita kasuwar ta yi tsammanin abubuwan nan ba za a kare su lafiya ba, domin masu sayen hannayen jari 'yan kasar waje sun sayar."

"Kafin zaben nan sai da kasuwar hannayen jari ta fadi da kashi 20 bisa 100 amma a ranar Laraba duk wannan hasarar da aka yi sai da aka mai da ta har ma aka shiga cikin riba," in ji Kurfi.

Ya kara da cewa an samu akalla ribar sama da naira biliyan 900.

Dagowar kasuwar dai ta jawo darajar naira ta karu idan aka kwatanta da dalar Amurka.