Ina tausaya wa Buhari-Sule Lamido

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido ya ce yana tausaya wa Buhari

Gwamnan jihar jigawa, Alhaji Sule Lamido ya ce yana tausaya wa Janar Muhammad Buhari dangane da irin rashin hakurin 'yan Najeriya ga shugabanninsu.

A wata hira da ya yi da wakilin BBC, gwamna Sule Lamidon ya ce matsalar 'yan Najeriya ita ce ta sha-yanzu-magani-yanzu abin da ya ce kuma ba haka al'amarin yake ba a gwamnatan ce.

Sai dai kuma ya taya janar Buharin murnar lashe zaben shugaban kasar da ya yi. Sannan ya yaba wa Buharin bisa maganganun da ya yi masu taushi wadanda suke nuni da aniyarsa na hadin-kan Najeriya.

Ya kuma jinjina wa shugaban kasa mai barin gado, Goodluck Jonathan bisa karbar sakamakon zaben da ya yi.

Alhaji Sule Lamidon ya ce hakan wajibi ne saboda irin yadda kasashen nahiyar Afirka suka damu da halin da Najeriyar ka iya fadawa idan da mutanen biyu ba su nuna dattako ba.