Ana tuhumar tsohon shugaban China

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Zhou Yongkang wanda ake tuhuma da cin hanci da rashawa

An tuhumi Daya daga cikin manyan tsoffin shugabanni a China da laifin bayar da cin hanci da kuma amfani da kujerarsa bata hanyar da ta dace ba.

Kamfanin dillacin labaru na gwamnatin China ya ce ana kuma zargin , da bayyana asirin gwamnati.

A bara ne dai hukumomin China suka tsare Mr Zhou, sannan suka kore shi daga jam'iyyar Communist.

Ba a dai sa ranar da za'a yi masa shari'ar ba , amma ya ce shari'ar zata kasance mafi mahimmanci a kasar cikin shekaru aru-aru.

Shugaba Xi Jinping dai ya dauki yaki da cin hanci da rashawa da muhimmanci a gwamnatinsa, amma masu suka sunce za'a iya amfani da wannan hanya domin cimma manufa ta siyasa.