Ghana ta samu lamunin dala miliyan 918

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugabar bankin bayar da lamuni na duniya IMF, Christine Lagarde

Shugabar bankin bayar da lamuni na duniya IMF, ta amince da bai wa Ghana bashin dala miliyan 918 a tsawon shekaru uku, domin taimaka mata samun habakar tattalin arziki, da samar da ayyukan yi da kuma daidaituwar al'amura.

Ghana za ta samu lamunin ne karkashin wani shirin bunkasa bayar da bashi domin bunkasa tattalin arzikinta da samar da ayyukan yi.

Manufar shirin dai shi ne farfado da dorewar bayar da bashi da inganta tattalin arziki da kuma cigaba.

Ghana za ta fara da karbar kimanin dala miliyan 114.8 daga cikin kudin nan ba da jimawa ba.