Iraqi: Za a kama masu kwasar ganima

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Iraqi a birnin Tikrit

Firai ministan Iraqi Haidar al-Abadi, ya ce za a kama dukkan wani wanda aka samu yana kwasar ganima a birnin Tikrit.

Umarnin da Mr al-Abadi ya bayar na zuwa ne yayin da rahotanni ke cewa ana ta kwasar ganima a gidajen da mutane suka gudu suka bari, tun bayan da dakarun gwamnati suka sake kwace iko daga hannun mayakan kungiyar IS a makon jiya.

Galibin mazauna birnin sun tsere ne daga cikinsa lokacin da gwamnati ta kaddamar da farmaki mafi girma ya zuwa yanzu a kan mayakan kungiyar ta IS.

An zargi mayakan sa-kai na Shi'a da taka muhimmiyar rawa a farmakin na gwamnati a Tikrit da kaddamar da hare-haren ramuwar gayya a kan mabiya Sunni.