Al Shabaab: An kama mutane biyar a Kenya

Image caption Jami'ai na ci gaba da gudanar da bincike kan harin

An cafke wasu mutane biyar a Kenya, da ake zargi da hannu wajen kisan da kungiyar Al Shabaab ta yi wa dalibai 148 a wata Jami'a a garin Garissa.

Kungiyar Al Shabaab ta fitar ta wata sanarwa tana mai ikirarin kara kai mummunan farmaki a kasar ta Kenya, inda ta ce ana gallazawa Musulmai.

Motocin safa sun fara jigilar daliban da suka tsira da ransu a harin zuwa gidajensu.

An gano wata daliba a ranar Asabar wadda ta buya a cikin wani kwabet na ajiyar kaya har na tsawon sa'oi 50.

Har yanzu wasu n ci gaba da neman 'yan uwansu da suke jami'ar lokacin da aka kai harin.

Javan Mwangi Mburu yana daya daga cikin masu neman 'yan uwan nasu, inda bai ji duriyar 'yar uwarsa, Mary Wanjiro Mushiri ba.

Ya ce '' Bayan da na kira wayarta da misalin karfe bakwai da rabi na safe sai da katse layin amma ta turo min da sako cewa ba za ta iya magana ba, kawai in taya su da addu'a. Har yanzu ban sake jin duriyarta ba.