An kama 'yan bindiga biyu a Kenya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'yan sanda sun cafke mutune biyu da ake zargin kai harin kan Garissa

'Yan sanda a kasar Kenya sun ce sun cafke mutane biyu wadanda ake zaton suna da alaka da harin da aka kai akan daliban jami'ar garin Garissa, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 150.

An dai samu mutanen ne a boye a cikin farfajiyar jami'ar.

Ana tsammanin daya daga cikinsu wadda mace ce ta kwashe awanni 24 tana boye a cikin wurin ajiyar kayan sawan daliban.

An kuma ce daya daga cikin mutanen biyu dan asalin kasar Tanzania ne kuma mai alaka da jami'ar. Sannan dukkannin su suna magana da harshe Swahili.

A yau ne kuma ake sa ran za a mayar da daliban zuwa jami'ar domin su kwaso kayansu kafin daga bisani a sada su da iyayensu.

Da safiyar ranar Alhamis ne dai 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Al-shabab ne suka kashe dalibai kimanin 148.