2015: Murnar da za ta cutar ta haramta- Malamai

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutane sun mutu a lokacin shagulgulan nasarar APC a Nigeria

A Najeriya a yayin da ake kokarin sake komawa runfunan zabe, wasu malamai da limamai a jahar Kaduna na nuna damuwa a bisa irin murnar da su ka gani a yayin da aka bada sanarwar cin zaben dan takarar jamiyyar APC na shugabancin kasar.

Malaman wadanda ke cewa murna ta halarta a musulunce sai dai su ka ce murnar da zata cutar da wani ta haramta.

Malaman sun ja hankalin 'yan kasa da su guji yin abubuwan da za su salwantar da rayukansu.

Rahotanni daga Nigeriar dai sun ce mutane da yawa sun mutu a lokacin bukukuwan murnar lashe zaben dan takarar jam'iyyar APC a zaben Shugaban Kasa Janar Muhammadu Buhari.

Rahotannin sun ce an yi ta wasa da ababen hawa da kuma tukin ganganci a titunan kasar.