'Yan bindiga sun kashe mutane 9 a Rivers

Hakkin mallakar hoto AFP

Yayin da ya rage sati daya a gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya, wasu 'yan bindiga a jihar Rivers sun kashe akalla mutane tara a wasu hare-haren da suka kai ma 'yan jam'iyyar APC a jihar.

Kakakin yan sanda a jihar, DSP Ahmad Muhammad, ya gaya wa Sashen Hausa na BBC 'yan bindigar sun kai hare-haren ne ranar Juma'a da daddare a yankunan Obrikom da Obor.

Ya ce 'yan bindigar sun kone gidan wani dan takarar mukamin kujerar majalisar dokoki a jihar a karkashin jam'iyyar APC.

Haka kuma sun kai farmaki a wani ofishin jam'iyyar APCn, su ka yi mashi kaca-kaca.

Babu dai wanda aka kama dangane da kai farmakin, amma kakakin 'yan sandan ya ce ana can ana kokarin kamo su.

Gwamnan jihar Rivers din dai dan jam'iyyar APC bayan ya fice daga jam'iyyar PDP ta Shugaba Goodluck Jonathan, wanda ya fadi zaben shugaban kasa amma ya samu kuri'u sosai a jihar.

Karin bayani