Ebola: Marayu na tsaka mai wuya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kungiyar ta ce ana mayar da yara saniyar ware, yayin da ake mayar da hankali wajen ceto rayuka kawai

Wata kungiyar agaji ta yi gargadin cewa yaran da cutar Ebola ta kashe iyayensu na fuskantar hadarin a manta da su yayin da yankin ke farfadowa daga annobar.

Wani sabon rahoto da kungiyar wadda ke aiki a yankin Afrika ta Yamma mai agazawa yara mai suna Street Child, da ke da cibiya a Birtania ta fitar ya nuna cewa, yara 25,000 ne a Afrika ya Yamma Ebola ta hallaka iyayensu.

Shugaban kungiyar, Tom Dannat, ya gaya wa BBC cewa, marayu da dama galibi mata, suna, sayar da jikinsu domin su ciyar da kansu.

Ya ce, ''a takaice, 'yan mata na da abin da za su sayar su rayu fiye da maza, kuma idan abu ya yi tsanani 'yan mata na sayar da kansu domin su da iyalansu su rayu.''