Gombe: APC ta zargi PDP da aron bakin Buhari

Hakkin mallakar hoto Getty

Reshen jam'iyyar APC a jihar Gombe ya zargi jam'iyyar PDP mai mulki da yin amfani da sunan janar Muhammad Buhari a yayin kamfe.

Wani jigo a jam'iyyar ta APC kuma tsohon gwamnan Gomben Alhaji Danjuma Goje ya shaida wa BBC cewa dan-takarar gwamnan jihar na PDP kuma gwamna mai-ci, Ibrahim Dan-Kwambo ya karaya, kuma ya na bi gari-gari yana cewa Buhari ya ce a zabe shi a matsayin gwamnan jihar domin idan ya ci zaben, zai koma APC.

Sai dai jam'iyyar ta PDP mai mulki a Gomben ta bayyana zargin da maras makama kuma ta ce farfaganda ce kawai ta siyasa.

Jam'iyyar APC ce dai ta lashe zaben Shugabancin Kasar.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan kafin a gudanar da zaben gwamnoni da 'yan majalisar jihohi da za a yi ranar 11 ga Afrilu na wannan shekarar.