Barayi sun kashe mutane 13 a Katsina

Hakkin mallakar hoto AP

Rahotanni daga jihar Katsina, a arewacin Najeriya, sun ce wasu 'yan bindiga da ake zargin cewa barayin shanu ne sun kashe akalla mutane 13 ranar Lahadi da yamma.

Lamarin dai ya faru ne a garin Shimfida da ke karamar hukumar Jibiya a jihar, inda a baya ma aka fuskanci irin wannan hari da ya haifar da asarar rayuka.

Wani mazaunin garin ya sheda wa Sashen Hausa na BBC cewa 'yan bindigar sun kashe mutanen ne a bakin garin.

Ya ce kuma yayin da aka je daukar gawawwakinsu, sai 'yan bindigar da suka yi kwanto bauna suka bude wa mutanen wuta, abinda ya janyo mutuwar jimlar mutane 13.

Sai dai ya ce har yanzu ba a kammala kwaso gawawwakin ba, an bari sai da safe saboda fargabar da ake da ita na kada a hadu da 'yan bindigar wajen dauko gawawwakin.

Kakakin 'yan sanda na jihar Katsinan ya sheda wa Sashen Hausa na BBC jami'ansu sun je wurin suna bincike, kuma da zarar sun kammala za su sanar da jama'a.

A baya dai yankin na Shimfida ya sha fama da hare-haren 'yan bindiga masu satar shanu.

Haka ma yankin Faskari ya jima yana fama da irin wadannan hare-haren, inda ko a watan jiya ma rahotanni suka ce an samu asarar rayuka a harin da 'yan binigar suka kai, kuma har ma aka samu mummunar musayar wuta tsakanin su da sojoji.

Karin bayani