Garissa: Majami'un Kenya sun yi addu'o'i

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An yi addu'o'i Easter a majami'u ga mutanen da aka kashe su 148

Kiristocin Kenya sun halarci bukukuwan Easter a majami'u a fadin kasar, inda suka yi addu'o'i ga wadanda harin da aka kai ranar Alhamis a kan Jami'ar Garissa ya shafa.

Da dama daga cikin majami'un dai sun yi mafani da masu gadi dauke da makamai don bayar da kariya ga masu ibada.

An yi addu'o'i ga mutane dari da arba'in da takwas, wadanda mayakan al-Shabab suka kashe; mayakan na al-Shabab dai sun ware wadanda ba Musulmi ba kafin su kashe su.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar ta daya daga cikin 'yan bindigar dan wani jami'in gwamnati ne a arewa maso gabashin kasar.

A cewar ma'aikatar, mahaifin yaron ya kai rahoton bacewar dan nasa lokacin da ake kai harin.

Karin bayani