An soma makokin kwanaki 3 a Kenya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Asibitoci sun karbi mutane da dama da su ka jikkata a harin

An soma makokin kwanaki uku a Kenya, bayan harin da mayakan al-Shabab suka kaddamar kan wata jami'a a garin Garissa, lamarin da yayi sanadiyar mutuwar mutane 150.

Shugaban Kenyan ya ce a lokacin makokin za'a sauko da tutocin kasar kasa-kasa

Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross a Kenyan ta ce ya zuwa yanzu, 'yan-uwa sun gano gawarwakin dalibai 50, a dakin ajiyar gawa dake birnin Nairobi.

Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenyan ya ce hukumomin Tsaro na kasar zasu kara matsa kaimi wajen yaki da kungiyar mayakan al-shabab

Jami'ar Al-Azhar ta birnin alkahira, ta yi allawadai da abinda ta kira harin ta'addanci da aka kai kan dalibai wadanda ba su ji ba , ba su gani ba.