INEC ta ce da na'urar tantance masu zabe za a yi zabe na gaba

Farfesa Attahiru Jega Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Hukumar Zabe ta Najeriya

Hukumar zabe ta kasa a Najeriya INEC, ta fitar da wata sanarwa inda ta jaddada cewar za ta yi amfani da Na'urar tantance katin masu zabe, wato Card Reader a turance - a zaben gwamnoni da 'yan majalisun dokokin jihohi da za a yi a ranar Asabar mai zuwa.

Hukumar zaben ta ce za a yi amfani da sashen dokar ka'idojin gudanar da zaben shekara ta dubu biyu da goma sha biyar da ya zayyana abinda za a yi idan na'urar tantance takin masu zaben ya ki aiki, kuma hukumar ba za ta iya maye gurbin ta a cikin wani lokacin da aka kayyade ba, alal misali na dage zaben zuwa rana ta gaba.

Haka nan kuma hukumar ta ce sassaucin da aka yiwa tanadin dokar a zaben 28 ga watan Maris na 2015 an yi sa ne kawai don zaben Shugaban kasa da na majalisar dokoki ta kasar da aka yi a wannan rana.

Sanarwar ta ce Hukumar ta kuma yi nazari a kan aiki da na'urar tantance katin masu zaben a zabukan ranar 28 ga watan na Maris sannan ta gano kalubalen da ak fuskanta sannan kuma ta dauki matakan da suka dace don magance su.