Mataimakin gwamnan Jigawa ya koma APC

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Masu lura da harkokin siyasa na ganin yanzu 'yan siyasa marassa akida za su yi ta komawa APC

A Nigeria, mataimakin gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Ahmad Mahmud ya koma jam'iyyar APC, kwana daya bayan da jam'iyyar PDP ta kore shi. Mataimakin gwamnan ya ce ya yanke wannan shawara ne bayan da jama'arsa suka dage cewa lalle sai ya koma APC. Taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar ta PDP a mazabar Galagamma ta mataimakin gwamnan shi ne ya kore shi ranar Lahadi, kuma reshen jam'iyyar a karamar hukumarsa ta Gumel ya amince da matakin.

Sai dai mataimakin gwamnan,ya ce daman tuni ya yanke shawarar barin jam'iyyar ta PDP kuma tsohuwar jam'iyyar tasa ta yi masa magiya da ka da ya fita amma ya ki. APC ce za ta kafa sabuwar gwamnatin tarayya a Najeriyar ranar 29 ga watan Mayu bayan da dan takararta Janar Muhamadu Buhari ya kayar da shugaba Jonathan na PDP a zaben ranar 28 ga watan Maris 2015.