Kenya ta kai hari a kan sansanin Al Shabaab

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wannan shi ne karon farko da Kenya ta kai wa Alshabaab hari tun bayan harin da aka kai Garissa a makon jiya.

Jiragen saman yaki na Kenya sun yi luguden wuta a kan sansanonin 'yan kungiyar al-Shabab a makwabciyar kasar, Somalia.

Kakakin rundunar sojin Kenya, David Obonyo, ya tabar da kai harin.

Ya kara da cewa jiragen yakin sun kai harin ne a sansanonin 'yan kungiyar ta al-Shabab guda biyu da ke yankin Gedo da ke kan iyakar Somalia da Kenya.

Wannan dai shi ne karon farko da dakarun Kenya ke kai wa 'yan al shabaab hari tun bayan harin da aka a jami'ar Garissa a makon jiya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 148.

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya sha alwashin daukar tsattsauran mataki a kan 'yan kungiyar masu tayar da kayar-bayan.

Kakakin rundunar sojin na Kenya ya shaida wa BBC cewa sojin sun mayar da martani a kan wata barazana da aka yi musu ranar Lahadi, inda suka kai hari a kan wani kauye.