Garissa: Kenya ta kare jami'an tsaronta

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An zargi jami'an tsaron Kenya da rashin daukar mataki da wuri.

Gwamnatin Kenya ta kare jami'an tsaronta bisa zargin da aka yi musu cewa sun ja-kafa a yunkurin da suke yi na dakile 'yan kungiyar Al Shabab lokacin da suka kai hari a jami'ar da ke Garissa ranar Alhamis.

Mutane a kalla 150 ne suka mutu sakamakon harin.

Kafafen watsa labarai na cikin kasar sun yi ta bayar da rahotannin da ke cewa jami'an tsaro na musamman sun shafe awowi da dama kafin su kai wa daliban dauki, haka kuma 'yan sanda ba su dauki mataki a kan daya daga cikin 'yan bindigar hudu da aka ba su labarinsa ba.

Sai dai mataimakin shugaban kasar, William Ruto, ya jinjina wa jami'an tsaron, yana mai cewa 'yan sanda sun je wurin da aka kai harin awa daya bayan kai shi.