Kenya ta mayar da martani kan al-Shabaab

Jirgin yakin kasar Kenya Hakkin mallakar hoto
Image caption Jirgin yakin kasar Kenya

Sojin Kenya sun ce jiragen saman yakinsu sun lalata sansanoni biyu da 'yan gwagwarmayar Islama ke amfani da su a Somalia sakamakon mummunan harin ranar alhamis da 'yan bindigar al-Shabaab suka kai a jami'ar Garissa.

Wannan shine matakin farko da kasar ta Kenya ta mayar a kan al Shabaab bayan harin da kungiyar ta kai da ya hallaka mutane 148 a Jami'ar Garissa

Kakakin sojin bai bayar da haske a kan ko wani ya mutu ko jikka ta daga ruwan bama baman a yankin Gedo ba.

To amma wani dan Somalia da ya shedi lamarin ya shedawa BBC cewar babu mayakan 'yan gwagwarmayar a yankin.

Ya ce bama baman su fada ne a kan rijiyoyi da kuma dabbobi.