Faransa ta ceto dan Holland a Mali

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kubutar da Mr Rijke ne a wani samame da aka kai.

Dakarun tsaron Faransa na musamman da ke Mali sun kubutar da dan kasar Holland din nan da aka sace a kasar shekaru uku da rabi da suka wuce.

Ma'aikatar tsaron Faransa da ke Paris ta ce an kubutar da Sjaak Rijke a lokacin wani farmaki da dakarun suka kai a arewacin Mali.

A cewar ma'aikatar an kama 'yan bindiga da dama lokacin da aka kai farmakin.

Har yanzu dai ba a san inda 'yan kasar ta Hollland guda biyu -- wadanda aka sace tare da Mr Rijke a watan Nuwanban shekarar 2011 a birnin Timbuktu -- suke ba.

An yi amannar cewa 'yan kungiyar al Qaeda ne suka sace Mr Rijke.