Jinsin zomaye suna bacewa a Brittaniya

Kungiyar masu sha'awar dabbibi a Brittaniya Hakkin mallakar hoto
Image caption Kungiyar masu sha'awar dabbibi a Brittaniya

Masana ilimin halittu sun yi kira ga jama'a su bayar da rahoto na ganin zomaye na daji da na gida a wani bangare na tattalin wannan jinsi na dabbobi.

A lokacin bazara, ba wuya a ga wadannan dabbobi lokacin da tsirrai a daji suka bushe sannan kuma zowa suna gab da haihuwa.

Kungiyar masu sha'awar dabbobi ta ce, mai yiwuwa zomayen na daji suna bacewa ne a Brittaniya a yayinda kuma zomayen gida wasu cututtuka masu yaduwa suka rinka kashe su.

An nemi mutane su aike da hotunan zomayen don taimakawa wajen farfado da zomayen da ake da su a kasar ta Ingila.

Dr Fiona Mathews wata babbar malama a sashen nazarin dabbobi kuma Shugabar kungiyar masu sha'awar dabbobi ta ce, "bayanan da muke da su kadan ne game da zomaye, don haka yana da muhimmanci mu san adadinsu yana karuwa ne ko ko yana raguwa".

Suna wani bangare ne na dabbobin da aka dogara da su, akwai dabbobi da dama dake cin su, ko dai ta wajen kiwo ko kuma a matsayin abinci ga irinsu dila da manyan tsuntsaye.

Tace, babu zomayen sosai a wasu yankuna na Ingila musamman wuraren da aka samu barkewar wata annobar cututtuka. Sai dai kuma a sauran wasu yankuna, sun yi yawa har ma sun zamo masu bannata amfanin gona.

Kungiyar masu sha'awar dabbobi tana bukatar mutane a dukkan sassan kasar su aike da rahotanni na ganin dabbobin nan musamman zomaye a yankunan karkara da suka hada da wuraren shakatawa da daji da kuma duwatsu.

Za a yi amfani da bayanan ne a cikin taswirar kasa ta dabbobi don tallafa ma matakai na tattalinsu nan gaba da kuma ayyukan bincike.

Derek Crawley wanda ke sa ido ga shirin taswirar ta kasa a Brittaniya ya ce za a iya gane bambancin zomayen na gida ne da daji ta hanyar bindinsu da yanayi.

Karin bayani