Turkiyya ta dage takunkumi kan shafukn sada zumunta

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Turkiyya da Amurka da EU sun ayyana kungiyar 'yan bindigar DHKP-C a matsayin ta 'yan ta'adda

An bude shafukan sada zumunta da muhawara na intanet a Turkiyya bayan da suka bi umarnin kotu na daina yada hotunan wani mai gabatar da kara da aka ritsa da bindiga.

An dage takunkumin toshe shafukan Facebook da Twitter bayan da suka bi umarnin.

Dangane da shafin Youtube kuwa rahotanni sun ce ana ci gaba da tattaunawa.

Rahotanni sun bayyana wasu 'yan bindiga biyu na wata kungiyar masu rajin kawo sauyi, sun yi garkuwa da mai gabatar da karar, a wata kotu a Istanbul.

Lamarin ya auku ne a makon da ya gabata.

Hakkin mallakar hoto EPA

Dukkanin mutanen uku sun mutu a kokarin kubutar da wanda aka yi garkuwa da shi.

Jami'an gwamnatin Turkiyya sun bayyana hoton na mai gabatar da karar Mehmet Selim Kiraz, da cewa farfaganda ce ta adawa da gwamnati.

Kafin toshe shafukan na intanet, hukumomin kasar sun hana jaridu buga hoton, bisa zargin cewa suna yada farfagandar 'yan ta'adda ta kungiyar DHKP-C