An yi batirin da zai yi caji a minti daya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Masana sun ce bitirin ba ya gurbata muhalli

Masana a birnin California na Amurka sun ce sun kirkiro wani batirin wayoyin komai-da-ruwan-kai, wanda zai rika yin caji cikin minti daya kacal.

Masanan da ke jami'ar Stanford sun ce an gina batirin ne da aluminium, kuma zai iya maye gurbin batiran da ake yin amfani da su yanzu.

Sun kara da cewa batirin da aka yi da aluminium ba ya gurbata muhalli kamar yadda batirin da aka yi da alkaline ke yi.

Kazalika batirin da aka yi da aluminium ya fi wanda aka yi da lithium, wanda ke kamawa da wuta.