Mutane sun fara komawa Gwoza

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A lokacin da mutane ke kaura daga Borno

Bayan kwanaki 12 da kwace garin Gwoza da rundunar sojin Nigeria ta yi daga hannun mayakan Boko Haram, wasu daga cikin wadanda su ka tsira sun bayyana artabun da su ka sha.

Tun bayan kwace garin dai wanda kungiyar Boko Haram ta mayar hedikwatarta, ba kasafai ake samun labarin abin da ke faruwa ba a can.

Kwanaki uku da suka wuce ne wani dan garin na Gwoza, wanda har lokacin da aka sake kwato garin yana boye a wani kogon dutse kusa da garin, da yanzu kuma ya samu isa sansanin 'yan gudun hijira na Maiduguri, ya shaida wa BBC wasu daga cikin irin abubuwan da suka faru da shi.

Mutumin -- wanda ya bukaci a boye sunansa ya ce "Yanzu haka akwai jami'an tsaro a kowanne sako na garin, kuma akwai mutane da su ka koma da dama musamman mata da yara."

Ya kuma ce su matasa suna boye a bayan garin Gwoza lokacin da sojoji su ka zo kwace garin "Sai 'yan Boko Haram din su ka umarci mata da yara da tsofaffi da su bar garin domin za su yi gumurzu da sojoji."

Mutumin ya tabbatar da cewa yanzu haka garin Gwoza na cikin lumana bayan fafatawar da aka yi inda sojojin su ka fatattaki mayakan Boko Haram, "na yi kimanin watanni tara ban ga mahaifana da iyalina ba shi yasa na taho."

A watan Agustan 2014 mayakan kungiyar Boko Haram su ka kwace ikon garin Gwoza inda su ka hallaka mutane da dama.