An yi zanga-zanga a ofishin INEC a Abuja

Image caption Masu zanga-zangar sun bukaci a cire shugabar hukumar zaben jihar.

Daruruwan 'yan jihar Rivers da ke kudancin Najeriya na yin zanga-zanga a ofishin hukumar zaben kasar da ke Abuja, inda suka bukaci a cire kwamishiniyar hukumar zaben jihar.

Masu zanga-zangar sun ce dole a cire kwamishiniyar, Gesila Khan, idan ana so a yi zaben gwamna cikin adalci da kwanciyar hankali ranar Asabar mai zuwa.

Sun zarge ta da hada baki da 'yan jam'iyyar PDP wajen yin magudi a zaben shugaban kasar da aka gudanar ranar 28 ga watan jiya.

A zaben dai, jam'iyyar ta PDP ta samu kuri'u 1,487,075, yayin da jam'iyyar APC ta samu kuri'u 69,238.

Gwamnan jihar, Rotimi Amaechi, wanda kuma shi ne daraktan yakin neman zaben dan datakar shugabancin kasar na jam'iyyar APC, ya yi zargin cewa an yi magudin zabe a jihar.

Sai dai dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar PDP, Wike Nyesom, wanda ke da goyon bayan matar shugaba Goodluck Jonathan, ya musanta zargin, yana mai cewa gwamnan yana yin soki-burutsu ne kawai.