An fara tono manyan kaburra a Iraki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu ramukan an yi su ne a gidan marigayi Saddam Hussein.

Ayarin masu binciken kwakwaf na Iraki ya fara tona wasu manyan ramuka da ake zargin an binne tarin mutane a cikinsu, a birnin Tikrit, kwanaki kadan bayan da aka kori mayakan kungiyar IS bayan wata daya da aka yi ta dauki-ba-dadin fatattakarsu.

Ana ganin cewa an binne gawarwakin sojin 'yan Shi'a ne su kusan 1,700, wadanda aka hallaka a watan Yuni da ya gabata, yayin da kungiyar ta IS ta kara mamaye yankuna a arewacin Iraqi.

Wasu daga cikin ramukan an yi su ne a gidan tsohon shugaban kasar ta Iraki, marigayi Saddam Hussein, inda mayakan na IS suka mayar shalkwatarsu a shekarar 2014.

Kisan kiyashin da aka yi wa sojojin na Shi'a -- wadanda aka kama a wajen sansanin sojin Amurka da ake kira Camp Speicher da ke kusa da Tikrit -- galibi ana ganin wata alama ce ta tsanar da mayakan IS suka yi wa 'yan Shi'a masu rinjaye.