Nyako: Babu baraka a APC kan mukamai

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Murtala Nyako ya ce akwai wasu manyan 'yan PDP a jihar Adamawa da suke shirin sauya sheka zuwa APC

Tsohon gwamnan jihar Adamawa da aka tsige, Vice Admiral Murtala Nyako ya ce babu gaskiya a hasashen cewa rabon mukamai na barazanar dusashe nasarar APC.

Tsohon gwamnan ya sheda wa BBC cewa, idan ma akwai wata matsala Janar Muhammadu Buhari yana da kwarewar aikin da zai magance ta.

Ya kuma ce jam'iyyarsu ta APC ta samu nasara a zaben shugaban kasa, saboda PDP ba ta rike kasar da amana ba.

Murtala Nyako, ya kara da cewa hakan ne ma ya sa kasar ta fada cikin matsalar tsaro da wahalhalu, wanda PDP ba ta nuna damuwa kan gyara ba.

Sannan ya ce a karkashin mulkinsu, suna sa ran hakan za ta kau, al'amura su dawo daidai.