Sabani tsakanin Obama da Netanyahu

Shugaba Obama na Amurka Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Obama na Amurka

Shugaba Obama ya yi watsi da bukatar Prime Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, cewa yarjejeniyar shirin nukiliyar Iran ta kasance da sharadin Iran ta amince da wanzuwar kasar Isra'ila.

A wata hira da aka yi da shi ta radio, Obama, ya ce, hakan zai kasance tamkar cewa Amurkan ba za ta kulla yarjejeniyar ba, har sai gwamnatin Iran ta sauya gaba daya, wanda ya ce hakan wani babban kuskure ne.

Tun da farko, wani jami'in gwamnatin Amurka ya ce,har yanzu ba a fayyace lokacin da za a cire wa Iran tarin takunkumin da aka sa ma ta ba, da zarar an cimma yarjejeniya ta karshe a kan shirin nukiliyar na Iran.

Karin bayani