Yau ce ranar kiwon lafiya ta duniya

Margaret Chat - Hukumar lafiya ta Duniya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Margaret Chat - Hukumar lafiya ta Duniya

Yau ce ranar kiwon lafiya ta duniya kuma taken bikin na bana shine kula da tsaftar abinci.

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya cin abinci maras kyau na haddasa mutuwar mutane akalla miliyan biyu a kowacce shekara ciki har da yara.

Hukumar ta ce cin abinci dake dauke da kwayoyin cuta ko sinadarai masu guba kan haddasa cututtuka kusan 200 kama daga amai da gudawa zuwa ciwon daji.

Karin bayani