Iran ta tura jiragen yaki kusa da ruwan Yemen

Image caption Jiragin ruwa na yaki

Iran ta aike da jiragen ruwa na yaki zuwa gabar tekun Aden.An ambato kwamandan dakarun ruwan Iran na cewa an aika jiragen ruwan na yaki ne domin su kare kasar daga 'yan fashi a cikin teku. Masu aiko da labarai sun ce aika jiragen ruwan na yaki zai janyo karuwar zaman dardar a yankin.

A yanzu haka dai Saudiyya na jagorantar sojojin kawance domin yakar 'yan tawayen 'yan shi'a a Yemen. Ana zargin cewar Iran ce ke goyon bayan 'yan shi'ar a Yemen. Ana kallon yunkurin Saudiyya a matsayin wani matakin rage karfin fada a ji na Iran a yankin.