Matan Afrika na fama da bakin talauci

Matan Afrika Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Matan Afrika

Kididdiga daga bangarori dabam-dabam dai na nuni da cewa Mata ne talauci ya fi addaba a kasashen Afirka, irinsu Najeriya, inda a kwanakin baya, wasu alkaluma daga ma'aikatar harkokin Mata ta kasar suka nuna fiye da kashi saba'in cikin dari na Matan kasar na fama da bakin talauci.

Sai dai ga alama wasu matan na himmatuwa domin kubuta daga kangin talaucin ta hanyar kama sana'o'i da kananan harkokin kasuwanci, Ko da yake dai suna fuskantar kalubale a irin fafutikar da suke yi.

Matan sun ce Shugabannin da aka zaba a yanzu suna da wani hakki mai girma na cetonsu daga halin da suke ciki.

Karin bayani