Babban Bankin Nigeria ya yi gargadi

Hakkin mallakar hoto Nigeria State House
Image caption Darajar Naira ta farfado

Babban Bankin Najeriya ya yi gargadi ga mutane da kungiyoyi da su guji yin amfani da kudaden kasashen waje domin yin saye da sayarwa a kasar.

A wata sanarwa da Babban Bankin ya fitar, ya ce ya gano cewa ana yin amfani da kudin kasashen waje-- musamman dalar Amurka-- wajen yin sayayya a kasar, yana mai cewa hakan ya sabawa dokar kasar.

Bankin ya yi gargadin cewa duk wanda aka kama yana sabawa dokar zai fuskanci hukuncin daurin watanni shida a gidan yari.

Rahotanni daga sassan kasar da dama dai na nuna cewa mutane na yin sayayya da kudaden kasashen waje, kuma lamarin yana shafar kimar kudin Najeriya, watau Naira.

A kwanan nan ne dai darajar Naira ya dan farfado, bayan faruwar da ta yi sakamakon faduwar farashin danyen man fetur da kuma sayen da ake yi wa kudaden kasashen waje ana boye wa.