Ana yunkurin tsige gwamnan Ekiti

Image caption 'Yan majalisun jam'iyyar PDP marasa rinjaye ke jan ragamar majalisar jihar Ekiti

'Yan majalisar dokoki 19 na jam'iyyar APC a jihar Ekiti, sun sha alwashin tsige gwamnan jihar Ayo Fayose.

Sai dai 'yan majalisar sun fuskanci tirjiya daga wasu matasa a wani kauye kusa da babban birnin a yayin da suke kokarin shiga garin a ranar Talata, inda har mutum daya ya rasa ransa.

A yanzu haka dai 'yan sanda na ci gaba da tsaron majalisar dokokin jihar ba tare da barin kowa ya shiga ba.

An dade ana takun saka tsakanin 'yan majalisar dokokin da gwamna Ayo Fayose a kan abubuwa da dama musamman kasancewar galibin 'yan majalisar 'yan jam'iyyar APC ne shi kuma gwamnan dan jam'iyyar PDP.

A yanzu haka dai yan majalisun da aka zaba karkashin jam'iyyar PDP ne ke jan ragamar jihar duk da yake su ne marasa rinyaje.

Yunkurin na baya-bayan nan na zuwa ne bayan da jam'iyyar APC ta lashe zaben shugaban kasa.