'Yan Somalia sun koka kan Kenya

Image caption Kenya ta ce matakin zai hana al-Shabaab samun kudi.

Al'umar Somali mazauna Kenya ta koka kan matakin da hukumomin Kenyan suka dauka na rufe hanyoyin aikewa da kudi guda 13 da suke amfani da su wajen aikewa da kudi gida.

'Yan Somalia mazauna Kenya na yin amfani da hanyoyin -- wadanda aka fi sani da hawalas -- domin aika kudi zuwa 'yan uwansu da ke Somalia, sai dai ana zargin cewa ana amfani da irin wadannan hanyoyi wajen kai wa 'yan ta'adda kudi.

Gwamnatin ta Kenya ta dauki wannan mataki ne bayan harin da 'yan kungiyar al-Shabaab na Somalia suka kai a jami'ar Garissa da ke Kenya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 150.

Kenya ta ce wannan zai toshe duk wata kafa da kungiyar al-Shabaab za ta samu kudin da taje yin amfani da su domin kai wasu hare-hare.

Tuni dai aka sanya dokar hana fita a wasu yankunan da 'yan Somalia mazauna Kenya suka fi yawa a arewacin kasar.

Kazalika, an rufe asusun bankunan mutane 86 da na wasu kugiyoyi da ake zargi suna daukar nauyin 'yan ta'adda.