Microsoft zai dauki masu cutar galhanga aiki

Hakkin mallakar hoto Stephen Brashear. Getty. Microsoft
Image caption Microsoft ya ce masu larurar za su samarwa kamfanin karfin da yake bukata

Babban kamfanin fasahar sadarwa na Microsoft zai dauki masu cutar galhanga (autism) aiki domin bunkasa ayyukansa.

Babban kamfanin na kayan fasaha zai fara shirin gwaji ne da daukar mutane goma a babban ofishinsa na Redmond.

Babban jami'a a kamfanin Mary Ellen Smith ta ce, ''mutane masu cutar galhanga za su samar da karfin da muke bukata a Microsoft.''

Kungiyar masu fama da cutar a Birtaniya (National Autistic Society), ta yi maraba da matakin.

Ta kuma ce kamata ya yi sauran kamfanoni su ma su yi hakan domin su amfana da kwarewar da masu cutar ke da ita.

Hakkin mallakar hoto video
Image caption Makahon mawaki Derek Paravicini, mai larurar galhanga

Da take bayyana sabon shirin ta intanet, Ms Smith ta ce, ''kowane mutum daban yake, wasu suna da baiwar haddace bayanai, wasu kuma a lissafi da makamantansu.''

kamfanin daukar ma'aikata na musamman, Specialisterne, shi zai taimaka a shirin.

Kamfanin wanda ke aiki a Denmark da Birtaniya, yana aiki da kamfanonin fasahar sadarwa da yawa da sauran fannoni, domin fito da kwarewar da mutane masu cutar galhanga ke da ita domin guraben ayyuka na musamman.

Sarah Lambert ta kungiyar masu cutar ta Birtaniya, ta ce abu ne mai karfafa gwiwa babban kamfani kamar Microsoft, ya fahimci muhimmancin amfanin kwarewar masu larurar.

Ta ce da dama masu matsalar suna da wata baiwa da za ta amfani ba kamfanin fasahar sadarwa ba kadai har ma sauran kamfanoni.