Sokoto: An sace sarkin Wamakko

Image caption Sarkin dan uwan gwamnan jihar Sokoto ne

Rahotanni daga jihar Sakkwato, a Najeriya, sun ce wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da sarkin gundumar Wamakko da ke jihar.

Bayanai sun ce 'yan bindigar wadanda ake jin masu garkuwa da mutane ne don neman kudin fansa su ne suka dauke Alhaji Salihu Baraden Wamakko da daren Laraba daga gidansa a garin Wamakko.

Basaraken dai yaya ne ga gwamnan jihar ta Sokoto da ke arewa maso gabashin kasar Alhaji Aliyu Magatakarda Wamakko.

A watan ranar 21 ga watan Maris da ya gabata ma wasu 'yan bindiga masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa suka sace sarkin Bukkuyum da ke jihar Zamfara, wanda suka sako shi bayan kwanaki.