Sabuwar hanyar yaki da wari sakamakon zufa

Turare na Musamman Hakkin mallakar hoto THINKSTOCK
Image caption Turare na Musamman

Masana kimiyya sun ce an bullo da wata sabuwar hanya ta sayar da turare wadda za ta tabbatar da cewa mutum yana kara yin kamshi a yayinda zufa ke kara barkowa daga jikinsa.

Masu bincike a Jami'ar Queens dake Belfast sun ware sinadaran dake sanya kamshi fitowa idan mutum ya yi zufa.

Suka ce, wannan wani tsari ne irinsa na farko da aka taba bullo da shi wanda ke aiki da ruwan dake fita daga cikin mutane idan suka yi zufa.

Cibiyar yada labarai ta masu harhada magunguna sun buga wannan sakamako na bincike.

An gwada tsarin ne ta hanyar zuba turare a kan wani ruwa na musamman mai gishiri wanda ba shi da wani wari.

Sakamakon dai ya nuna turaren ya saki wani irin kamshi a lokacinda aka hada shi da wannan ruwan, abinda zai sanya turaren kamshi kenan idan aka shafa shi ga fatar jikin mutum.

Daya daga cikin masu binciken Nimal Gunarante daga sashen bincike na Jami'ar ta Queens ya ce abinda aka fi sani da "kamshin" kamar wani sinadari ne wanda ba zai gushe ba, ya kara da cewa an cire abinda ya hada su lokacinda aka zuba wannan ruwan.

Ya gaya ma shafin labarai ta internet na BBC cewar, "ruwa kamar almakashi ne".

Tsarin turaren yana kuma da wani abu da zai iya cire warin maras dadi wanda ke fitowa daga jibin da mutane ke yi.

Sinadaran dake sanya wannan warin suna, suna haduwa da wannan ruwan dake mannewa a jikin fata.

A lokacinda suka hadu, karfi da tasirinsu ya kan dushe.

Masu binciken suka ce sakamakon zai yi tasiri ta fuskar huddar kasuwanci, suna kuma aiki da wani kamfani don gano irin kayan da za a rinka yi a tsarin bukatunsu.

Karin bayani