An samu Dzhokhar Tsarnaev da laifin kisan kai

Dzhokhar Tsarnaev Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutumin da aka samu da laifin harin Boston na 2013

Mutumin nan da ke zargi da kai harin bam a gudun famfalaki na Boston a shekarar 2013 , an same shi da laifin amfani da makamin kare dangi da ya yi sanadiyar mutuwar mutane.

Bayan da masu taya alkali yanke hukunci suka shafe sa'o'i goma sha daya suna tattaunawa, sun kuma sami Jaha Zanayev da laifin hada baki don amfani da makamin kare dangi.

Dukkanin laifukan biyu za'a iya yanke wanda ake zargi hukuncin kisa.

Wakilin BBC ya ce Jiha Zannayev ya sa tukunyar iskar gas da ake girka abinci a wurin da akwai cunkuson jama'a kusa da yara yan makaranta.

Kuma hotunan bidiyo da aka dauka daga wurin da lamarin ya faru sun nun cewa be nuna ya damu , ganin irin jinin da zai zubar ba.