Kungiyar IS ta kai hari kan gidan talabijin a Faransa.

Image caption IS ta kai hari TV5-Monde

Gidan talabijin mai yada labaran duniya a Faransa, mai suna TV5 -Monde na ta kokarin dawo da ayyukan yada labaransa a dukan kafofinsa, bayan da wasu da suke ikirarin 'yan kungiyar IS ne, suka yi kutse a gidan talabijin din.

Daraktan kamfanin, Yves Bigot, ya ce, harin ya yi tasiri sosai kuma ana ganin cewar abu ne da aka dauki tsawon lokaci ana shirya shi.

Ya ce "An ci gaba da aikace-aikacen yada labarai, sai dai kuma wadanda aka dauka ne kawai ake iya yadawa."

Fira ministan Faransa, Manuel Valls, ya ce wannan hari ne a kan 'yancin yada labarai da kuma bayyana ra'ayoyi.

A lokacin da lamarin ya faru, a shafin farko na gidan talabijin din an wallafa wani sako daga wata kungiya mai kiran kanta 'Cybercaliphate' inda ta rubuta " ni I-S ne".