Dan bindiga ya bude wuta a kotun Milan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mutane hudu aka kashe a harin na kotun Milan

Wani dan bindiga a birnin Milan na kasar Italiya ya bude wuta a cikin wata kotu inda ya kashe alkali da kuma wani lauya.

'Yan sanda sun ce dan bindigar wanda ake yi wa shari'a kan karayar arziki, ya ranta ana kare bayan harbe-harben da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudu.

Ministan harkokin cikin gidan Italiya, Angelino Alfano ya ce bayan da dan bindigar ya yi aika-aikar, sai ya boye a cikin wani gini kafin ya gudu a kan babur.

Daga bisani an damke shi a yankin arewacin Milan.

Ganau sun bayyana yadda lauyoyi suka yi ta gudun neman tsira lokacin da lamarin ya faru.