'Yan siyasa na tururuwar komawa APC

Tun bayan da aka sanar da Janar Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa a Nigeria, manyan 'yan siyasar kasar ke ta rububin koma wa jam'iyyar APC.

A yanzu haka dai jiga-jigan jam'iyyar PDP wacce ta mulki kasar tun daga shekarar 1999, su ne kan gaba wajen sauya sheka zuwa jam'iyyar APC wacce za ta soma jan ragamar kasar daga ranar 29 ga watan Mayun bana.

Na baya-bayan nan shi ne wani dan kwamitin yakin neman zaben shugaba Goodluck Jonathan, Alhaji Isa Tafida Mafindi wanda ya ce ya sauya sheka ne saboda jam'iyyar PDP ta yi mutuwar kwando.

da wasu jiga-jigan PDP a jihar Adamawa kamarsu Sanata Jonathan Zwingina duk sun koma APC.

A jihar Jigawa ma, mataimakin gwamnan jihar da wasu manyan jami'an gwamnatin Sule Lamido duk sun koma jam'iyyar APC.

Sai dai tsohon mai bai wa Shugaba Jonathan shawara kan harkokin siyasa, Barrister Ahmed Gulak ya ce Allah Ya raka taki gona kuma matakin ba zai rage tagomashin jam'iyyar PDP ba.

Masu sharhi na kallon matakin na sauya sheka bayan zaben shugaban kasa a matsayin wata alama ta rashin akida a siyasar Nigeria.