Falasdinawa za su yaki IS tare da Syria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sansanin 'yan gudun Hijrah.

Falasdinawa sun amince su yi aiki tare da gwamnatin Syria domin fatattakar mayakan kungiyar IS, daga sansanin 'yan gudun hijira da ke Yarmouk a wajen birnin Damascus.

Wani babban jami'in hukumomin Falasdinu da ke gabar yamma da kogin Jordan ne ya ba da wannan sanarwar.

'Yan kungiyar IS sun kaddamar da hari a sansanin a wannan makon, inda suka ci karfin sansannin duk da tirjiyar da suka fuskanta daga mayakan sa-kai Falasdinawa.

A kalla 'yan gudun hijira 18,000 suna cikin wannan sansanin, kuma suna fuskantar karancin abubuwan more rayuwa.

Kafin a soma yakin basasar Syria, sansanin Yarmouk na da 'yan gudun hijira fiye da 150,000 kuma akwai masallatai da makarantu da kuma gine-ginen gwamnati.