Ficewa daga PDP kuskure ne - Gulak

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Barister Gulak ya ce babu gudu ba ja-da baya

Wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar PDP a Nigeria sun fara mayar da martani game da sauya-shekar da wasu 'ya'yanta ke yi a fadin kasar zuwa jam'iyyar APC.

Tun bayan kayen da jam'iyar PDP ta sha a zaben shugaban kasa, wasu 'ya'yanta ke yi kaura zuwa APC, ciki har da tsaffin gwamnoni da sanatoci da kuma 'yan majalisar wakilai.

Tsohon mai bai wa shugaban kasar shawara a kan harkokin siyasa, Barrister Ahmed Gulak, a hirarsa da BBC ya ce wadanda ke wannan sauya shekar sun yi kuskure.

"Kawai don an yi karo sau guda sai kace ka bar jam'iyya, ai ba daidai bane. 'Yan PDP masu kaunarta bai kamata su bar jam'iyyar ba domin za a kara farfado da ita," in ji Gulak.

Ya kara da cewa "Za ku sha mamaki nan da watanni shida zuwa shekara daya masu zuwa, jam'iyyar PDP za ta dawo sabuwa kar, kuma da karfin doki. Ina nan daram a PDP ba inda zani."