Turkey ta yi barazanar rufe shafin Google

Shafukkan Internet a Turkiyya Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shafukkan Internet a Turkiyya

Kasar Turkiyya ta yi barazanar haramta kafar shiga shafin Google a kasar muddin ta ki cire kafofin kai wa ga hotunan wani mai gabatar da kara wanda aka yi garkuwa da shi da bakin-bidiga.

A makon jiya ne aka dauki hotunan a lokacinda aka mamayi wata Kotu a Istambul lokacinda wasu 'yan bidiga biyu suka yi garkuwa da mai gabatar kara na kotun. Dukkan mutanen ukku dai sun mutu a lokacinda aka yi kokarin ceton sa.

An janye barazanar ne a kan Google lokacinda kamfanin na Internet ya janye dukkan kafofin kaiwa ga sashen da aka sanya hotunan.

Hukumomin Turkiyya sun toshe wasu kafofi na sada zumunta na wani dan takaitaccen lokaci a wani yunkuri na hana yaduwar hotunan.

A ranar 6 ga watan Aprilu, wata Kotu a kasar Turkiyyar ta umurci kamfanonin dake hada mutane da internet a kasar su toshe kafofin shiga shafukkan sada zumunta na Youtube da Twitter da Facebook da kuma wasu shafukkan sama da 160 wadanda ke ba mutane kafar tura ma wasu mutanen hotunan da ake magana a kan su.

Sun nuna mai gabatar da kara na Kotun Mehmet Selim Kiraz da wani mahari da ya lullube fuskarsa - tsaye a kansa, ya auna masa bindiga ga goshi.

An yi garkuwa da Mr Kiraz ne saboda ya jagoranci wani bincike da aka yi a kan mutuwar wani yaro a shekara ta 2013 lokacinda aka yi wata zanga-zanga ta nuna kin jinin gwamnati.

Maharan biyu wadanda suka yi garkuwar da Mr Kiraz ana kyautata zaton magoya bayan jam'iyyar DHKP-C ne ta masu ra'ayin kawo sauyi. Mr Kiraz da maharan sun mutu ne a musayar wuta da aka yi da 'yan sanda a wani yunkuri na kawo karshen Kawanyar da suka yi ma yankin.

Zuwa yammacin ranar litinin, an janye matakin da aka dauka na toshe kafofin shiga shafukkan na sada zumunta bayan sun daidaita, an kuma janye hotunan da aka sanya wadanda ke zagaye a shafin na Internet.

Karin bayani