Kasashe da dama sun kasa cimma buri kan Ilimi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Rahoton ya ce Najeriya da Nijar da kuma Chadi sun gaza wajen cimma burin

Majalisar dinkin duniya ta ce rabin kasashen duniya ne kadai suka cimma burin sanya dukkanin yara a makarantun faramare zuwa shekaran nan ta 2015.

Rahoton da hukumar kula da ilimi da kimiyya da kuma al'adu ta majalisar, watau UNESCO, ta fitar, ya nuna cewa, har yanzu kusan yara miliyan 60 ne ba sa samun ilimi samsam.

Kasashen da rahoton ya ware, domin yaba musu kan kokarin da suka yi, sun hada da Afghanistan da Nepal da Saliyo da Ruwanda da Tanzania da kuma India.

Hukumar ta ce kasashen da ke da sauran tafiya mai tsawo wajen cimma burin sun hada da Najeriya da Nijar da Chadi da Habasha da kuma Pakistan.

An dai kara sanya wa'adin zuwa shekara ta 2030 domin cimma burin samar da ilimin ga dukkanin yara, kuma hukumar ta UNESCO ta ce ana bukatar karin dala mliyan dubu 20 a shekara domin samun nasara.